Wata sanarwar offishin minstan cikin gida na Taiwan ta ce, ci gaba da yin barazanar na sojojin China zai iya haifar da tashin hankali da tabarbarewar tsaro a yankin. Ma’aikatar cikin gidan ta Taiwan ta yi gargadin, tana mai kira ga hukumomin

China da su dakatar da wadannan munanan ayyuka da suka kira tsokana. Tun a shekara ta 1949 kasashen biyu ke yin rikiciwandaChina ta yi ikirarin cewar yankin mallakarta ne.