An Kai Sabon Hari a Kudancin Kaduna


 

Duk da dokar ta baci da gwamnatin jahar Kaduna ta sanya, an kai wani sabon hari a kauyen Goskan da ke gefen garin Kafanchan a Cikin karamar hukumar Jema’a da ke jahar Kaduna.

Rahotanni na nuna cewa harin ya haddasa rasuwar mutane biyar wadanda yawancinsu mata ne.

Gwamnatin jahar ta Kaduna dama dai ta kakaba dokar-ta-bacin ne a kananan hukumomin uku da ke kudancin jahar tare da tura sojoji saboda irin wannan bacin rana a sakamakon rikicin da ya barke a garin Kafanchan a karshen makon da ya gabata.

Tuni dai Gwamnan jahar, Malam Nasir El Rufa’i ya yi Allah wadai da harin inda ya yi alwashin ganin cewa an cafko miyagun da suka aikata shi.

Ya kuma jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu wanda a ciki har da tsohon shugaban karamar hukumar Jema’a, Gidieon Morik wanda ya rasa diyarsa a harin.

You may also like