An kai wa wasu dalibai mata hari a wasu jami’o’in Amurka


kanadada_basortusu_ayari

 

An kai wa wasu dalibai mata 2 hari a jami’ar San Diego da ke jihar California ta Amurka.

Al’amari na farko ya afku ne a jami’ar gwamnati da ke San Diego.

Sanarwar da ofishin ‘yan sandan jami’ar ya fitar na cewa, wasu dalibai maza ne suka kai wa matan hari saboda bayyana ra’ayinsu game da shugabancin Amurka da kyma zabar Donald Trump.

Sanarwar ta ce, babu wani abu da ya samu dalibai matan, kuma maharan sun kwace motar daliba 1 tare da guduwa.

Shugabar jami’ar Elliot Hirshman ta soki harin inda ta yi gargadi da cewa, wannan abu na iya shafar ruhun hadin kan jami’ar.

‘Yan sanda sun fara gudanar da bincike game da wannan lamari.

Daya harin kuma ya afku ne a jami’ar San Jose.

Dalibar da aka kai wa harin Esra Altun ta sanar da manema labarai cewa, a dai-dai lokacinda ta ke kokarin shiga motarta a hawa na 3 na gurin ajje motoci ne wani ya zo ta bayanta ya ja dankwali da kuma gashinta.

Ta ce, bayan wasu saniyoyi ne maharan ya tafi ba tare da ce mata komai ba.

Altun ta ce, maharin ya yi mata haka ne saboda kyamar Musulmi kuma ta ja hankali kan yadda abin ya faru kwana 1 bayan zabar Donald Trump a matsayin shugaban kasa.

Trump dai ya sake rura wutar rikicin nuna wariya da kyamar Musulmi a Amurka.

You may also like