An kai wa wata Kamfanin Man mallakin kasar Italiya hari a Najeriya


 

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai wa jami’an tsaron wata Kamfanin Man fetur mallakin kasar Italiya hari a kudancin Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran kasar Faransa ya nakalto magabatan yankin da Jami’an tsaron Najeriya a wannan Laraba na cewa Wasu ‘yan bindiga da ba san ko su waye ba sun kai wa Jami’an tsaron wani kamfanin Man fetur mallakin kasar Italiya watau ENI hari, inda suka kashe jami’an tsaro guda 4 tare da jikkata wasu na daban daga cikin su.

Rahoton ya ce harin ya auku ne a kusa da tsibirin Fatakol mai arzikin man fetur na jihar Rives dake kudancin Najeriya, ya zuwa yanzu babu wani gungu da ya dauki alhakin kai wannan hari.

Daga farkon shekarar 2016 zuwa yanzu, tsagerun Niger-Delta sun kai hare-hare da dama kan bututun Man fetur na kasar da kuma na kamfanonin kasashen waje kamar Shell, ENi da saurensu.

You may also like