An kai wa wasu ‘yan sanda 2 hari da wuka a ciki da wuyansu a Brussels babban birnin kasar Beljiyom.
An samu nasarar kubutar da ‘yan sandan amma kuma sun samu raunuka kadan.
An harbi maharin da ya yi kokarin guduwa tare da kama shi.
A shekarar 1973 aka haifi maharin mai suna Hitcham kuma dan asalin kasar ta Beljiyom ne.
A gefe guda kuma jami’an tsaro sund auke wani kundhin leda da aka samu a tashar jirgin kasa ta birnin.
Binciken da aka yi ya nuna cewa, babu wani na fashewa a cikin ledar.
A watan maris din da ya gabata mutane 32 ne suka mutu sakamakon harin daaka kai a birnin Brussels.
Kasar dai na cikin fargabar barazanar ‘yan ta’adda.