
Asalin hoton, Senate Facebook
Kan ƴan majalisar dattawan Najeriya ya rabu biyu kan batun sabbin ƙa’idojin da babban bankin ƙsar CBN, ya fitar na ƙayyade cire kuɗaɗe.
Hakan ya faru ne a yayin gabatar da rahoton kwamitin da ke lura da sha’anin banki na majalisar dattijan kan sabbin tsare-tsaren da ka’idojin CBN din.
Wasu mambobin majalisar sun nuna goyon bayan tsarin na CBN yayin da wasu kuma suka nuna ƙin amincewa da sabbin ƙa’idoji cire kuɗaɗen.
Shugaban kwamitin Sanata Uba Sani ne ya gabatar da wannan rahoto a zaman da majalisar ta yi na ranar Laraba.
Ƴan majalisar sun shafe tsawon sa’a’o’i suna tafka muhawara a kan batun.
Sanata Uba Sani ya gabatar da rahoton mai cike da rudani, wanda kuma ‘yan majalisar suka yi ta jayayya akai.
A karshe an buƙaci a bayar da lokaci domin sake nazari kan shawarwarin da majalisar ta bayar.
Sanata Adamu Alero na daga cikin wadanda suka goyi bayan wannan sabbin ƙa’idoji.
“Ina ganin abin nan yana da amfani ga jama’a, kuma zai hana sayen ƙuri’a da kuɗi. Zai ragebayar da kuɗaɗe ga masu jefa ƙuri’a, kuma zai kawo tsafta ga siyasarmu.
“Saboda me? Saboda siyasar da ake yi ta kudi za ta rage har a zaɓi shugabanni kan cancantarsu ba saboda kuɗin da za su bayar ba.
“Ni na yi na’am da hakan. Idan kana da jama’a kuma suna sonka ka musu alheri ka mutunta su, to za a zabe ka. Idan kuma ba ka yi ba, ka ajiye kudi ko ka saci kudi don ka bai wa mutane, to kudin ba zai samu ba,”in ji shi.
Asalin hoton, Senate
Sanata Bulkacuwa ya ce tsarin bai dace a yanayin da Najeriya ke ciki a yanzu ba
Shi kuwa Sanata Adamu Muhammad Bulkacuwa daga Bauchi ta Arewa, ya ce akwai abubuwa da dama da aka bari a baya kafin aiwatar da waɗannan dokoki.
“Ainihin gundarin tsarin idan har mun kai lokaci to yana da kyau, duk ƙasashen da suka ci gaba suna yin hakan.
“Amma a inda muke a yanzu a Najeriya, d ayadda tattalin arzikinmu yake to ba mu kai ba, a cewar Sanata Bulkachuwa.
Ya jadda cewa ƙasashen da suka ci gaba suna da wadatatun hanyoyin bin tsari, “yanzu a ƙasashen waje da suke yin wannan, ba za ka yi tafiyar kilomita 10 ba tare da ka samu banki ba.
“Amma mu a Najeriya, amazaɓata gaba ɗaya ƙananan hukumomi bakwai ne, amma a ƙananan hukumomi biyu ne kawai ake da banki . Saboda haka ni ina ga tsarin bai dace da mutanenmu na ƙauye ba.”
Shawarwarin da ƴan majalisar suka bai wa CBN
Ƴan majalisar dai sun bai wa babban bankin Najeriya shawarwari uku, amma waɗanda suka amince da rahoton sun yi watsi da ɗaya suka kuma amince su yi amfani da biyu.
Na farko dai a cewarsu ya kamata a sake nazari kan wannan ƙa’idoji.
Na biyu kuma shi ne bayar da cikakken lokaci ga ƴan Najeriya domin fahimta da kuma sabawa da waɗannan sabbin ƙa’idoji da babban banki ya bijiro da su.