Kakakin tsohon Shugaban Kasa, Janar Ibrahim Babangida( IBB), Mista Kassim Afegbua ya maka Sufeto Janar na ‘yan sanda, Ibrahim Idris kotu bisa bayyana shi a matsayin wanda rundunar ke nema ruwa a jallo kan fitar da wata wasikar karya inda a ciki ya nuna cewa IBB ya ja kunnen Shugaba Buhari kan ya jingine batun yin tazarce.
Mista Afegbua ya ce, rundunar ‘yan sandan ba ta gayyace shi sai dai kawai ta nuna tana nemansa ruwa a jallo don haka ya nemi kotu ta tilasta rundunar kan ta biya shi diyyar Naira Bilyan daya bisa abinda ya kira da bata masa suna. Haka ma, ya tabbatarwa kotu kan cewa a yau ne zai kai kansa ga ‘yan sanda don amsa tuhumar da ake yi masa na kokarin tayar da hankali kan fitar da wasikar.