Kalaman Ban Tsoro Da Mamaki Daga Aisha Buhari. 


“Mai girma shugaban kasa ya dauki mukamai ya bawa wadanda ko katin zabe ba su da shi ballantana ace sun zabe shi. Kuma suna ta amfani da kudaden ‘yan Nijeriya suna ta Fantamawa abin su. Amma an bar talakawan da su kai ruwa su kai tsaki, suka sha rana wajen tabbatuwar gwamnatin suna ta fama da da tsadar rayuwa da yunwa da matsanancin talauci”.
Kadan kenan Mai girma shugaban kasa ya dauki mukamai ya bawa wadanda ko katin zabe ba su da shi ballantana ace sun zabe shi. Kuma suna ta amfani da kudaden ‘yan Nijeriya suna ta Fantamawa abin su. Amma an bar talakawan da suka ruwa suka yi tsaki, suka sha rana wajen tabbatuwar gwamnatin suna ta fama da da tsadar rayuwa da yunwa da matsanancin talauci.

cikin hirar da sashen Hausa na BBC ya sanya a yau Talata 11/10/16 tare da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari. Nasiru Salisu Zango dan Jarida mai fafutukar kwato hakkin talakawa da ke jihar Kano, ya girgiza matukar gaske da sauraron wannan hira. ” Ta tsima ni, idan abin da na ji haka yake akwai matsala, domin a cikin kalaman ta naji tana cewa, abin da take tsoro shine boren mutane miliyan 12, amma a karshe tace ta yanke hukunci sai nan gaba za a ji irin hukuncin da ta yanke…..Wannan hira tana kunshe da abubuwa masu ban tsoro da ban mamaki”.

Zuwa yanzu ‘yan Nijeriya sun kasa sun kuma tsare domin jin ragowar tattaunawar daga BBC HAUSA.

You may also like