KALAMAN MATAIMAKINA SUN GIRGIZANI SOSAI – GANDUJE Gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana cewa, yayi matukar kaduwa da kalaman mataimakin sa Farfesa Hafiz Abubakar, dangane da cire shugaban jam’iyyar Mandawari. Ba tare da bata lokaci ba Ganduje ya yi umarnin gaggauta mayar da shugaban mazabar. Kana kuma ya nemi ‘yan siyasa da su rika tuntubar shugabanni kafin yanke hukunci. 
A karshe ya nemi ‘yan jam’iyyar APC da su girmama mataimakin sa domin samun zaman lafiya da hadin kan jam’iyyar.

You may also like