Rundunar tsaro na farin kaya ta nuna cewa ta samu motocin Alfarma har 18 a gidan daya daga cikin Alkalan da jami’anta suka kama bayan kayayyakin Alfarma na gida da ya sayo daga kasashen Brazil da Dubai wadanda aka zuba a cikin sabon gidan da ya gina.
A bangare daya kuma, Ministan Shari’a, Abubakar Malami ya nuna cewa matakin kama Alkalan bai saba doka saboda a cewarsa babu wanda ya fi karfin doka idan har an same shi da aikata miyagun laifuka na cin hanci da rashawa.
Sai dai kuma majalisun tarayya sun yi Allah-wadai da matakin kama Alkalan inda suka nuna cewa ya kamata gwamnatin ta mutunta bangaren shari’a a matsayin mai cin gashin kansa kuma cewa akwai hukumar kula da kotuna wadda ita ce doka ya ba ikon hukunta duk wani alkali da aka samu da laifi.