Tsohon Shugaban Kasa, Yakubu Gowon ya yi ikirarin cewa matakin da jami’an tsaro suka dauka na kama wasu manyan Alkalai ba karamin barazana ba ne ga tsarin mulkin dimokradiyya.
Ya kalubalanci gwamnatin kan ta rika bayar da umarni ga jami’an tsaro bisa tsarin mutunta doka ta yadda ba za su shiga hurumin da ba nasu ba.