Kama Alkalai: Kungiyar Lauyoyin Nijeriya Ta yi Amai Ta Lashe


 

 

 

 

Bayan da ta yi Allah wadai da sumamen da hukumar DSS ta kai wa wasu alkalan Nijeriya ‘yan kwanakin da suka gabata a sakamakon zargin su da ake yi da aikata laifin cin hanci da rashawa, sai gashi kuma kungiyar lauyoyi ta Nijeriya NJC ta lashe aman ta, ta bukaci dakatar da Alkalan da ake zargi da karbar cin hancin.

Shugaban kungiyar, Mahmoud Abubakar (SAN) shi ya yi wannan kira a wajen bikin girmamawa ga Mai shari’a Sotonye Denton-West, daya daga cikin alkalan daukaka kara da ke Abuja, wacce ta yi ritaya.

Mahmoud ya bayarda dalilinsa na yin wannan kira da cewa dole ne kungiyar ta kare martabar fannin shari’a da kotuna, ta kuma dawo da kimarsu a idon ‘yan Nijeriya.

Ya kuma ce zai fi kyautuwa idan hukumar ta dakatar da alkalan har sai sun iya wanke kansu daga laifukan da ake zarginsu da shi.

Wannan magana dai ta sha ban-ban da matsayar kungiyar ta farko, inda ta caccaki hukumar ta DSS, ta kira sumamen da ta kaiwa mambobinta da cin zarafi, har ma ta kaddamar da dokar ta baci a bangaren shari’a na kasar.

A makon da ya gabata ne dai hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi sumame zuwa gidajen wasu manyan alkalan kasar da suka hada da na kotunan koli da na manyan kotuna, inda ta bayyana nasarar samun miliyoyin kudade a gidajen alkalan da ake zargi sun karbi cin hanci.

Manyan masana shari’a a Nijeriya dai na ci gaba da bayyana goyan bayansu na tsaftace bangaren shari’ar kasar.

You may also like