An kama bakin haure 816 a Sudan ta Kudu


 

 

migrants_mali_0

 

 

 

Jami’an tsaro a kasar Sudan sun kama baki yan kasashen Afirka 816 akan iyakar kasar da Libiya wandanda ke kokarin tsallakawa nahiyar Turai cikin watanni biyu da suka gabata.

Jami’an sun bayyana cewar 347 daga cikin su sun fito ne daga kasar Eritrea, 130 daga kasar Habasha yayinda 90 kuma yan kasar Sudan ne.

Mai Magana da yawun rundunar sojin kasar, Janar Aseer Hussein Bashir, yace sun rasa sojojin su guda biyu wajen fafatawa da masu safarar bakin, kuma sun kama 10 daga cikin su.

Matsalar safarar mutane zuwa nahiyar turai ta zama ruwan dare a nahiyar Afrika duk da kokarin da hukumomi ke yin a dakile hakan, abinda akafi dangatawa da talauci ke haifar da kara ta’azzarar matsalar.

 

You may also like