An kama Faston da sanya wa ɗansa sasari


‘Yan Nigeria suna ci gaba da bayyana ra’ayoyinsu dangane da wani yaro dan shekara tara da jami’an tsaro suka ceto bayan mahaifinsa ya sanya shi cikin sasari saboda zargin cewa yana yin sata.

Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun da ke kudu-maso-yammacin kasar ta ce ta kama mahaifin yaron, wanda limamin wani Coci ne.

Mahaifin yaron, mai suna Francis Taiwo, wadda Fasto ne a Cocin Key of Joy Celestial Church, ya zargi dan nasa cewa yana yin sata, matsalar da ya ce za ta yi wa rayuwarsa illa a nan gaba.

Ya dai bayyana hakan ne lokacin da ‘yan sanda ke yi masa tambayoyi, yana jaddada cewa dan nasa na fama da wasu aljanu da ke saka shi sace-sace.

A cewarsa, baya tare da mahaifiyar yaro, wadda ya ce ta haifa masa yara hudu, amma sun rabu tun a shekara ta 2007.

‘Yan sanda sun ce za su gurfanar da Faston gaban kuliya da zarar sun kammala gudanar da bincike.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like