An Kama Mai Maganin Gargajiya da Sassan Jikin Mutane


 

native-doctor

 

 

Rundunar ‘yan sandan jahar Abia ta cafke wani mutum mai shekaru 28 dauke da sassan jikin mutane, bayan da mutanen unguwar da yake suka yi masa shune.

Kwamishinan ‘yan sandan jahar Leye Oyebade ya fadawa manema labarai a garin Umuahia a jiya Talata cewa an kama mutumin ne domin ya mallaki kashin kai da na wasu sassa na jikin mutum.

 

Ya kara da cewa mutumin ya kasa yin gamsasshen bayani game da yadda ya samu kasusuwan a yayin da ake masa tambayoyi.

Oyebade ya ce suna kyautata zaton cewa an samu kasusuwan ne bayan da aka kashe mutum.

Sai dai mutumin ya musanta wannan batu inda ya ce marigayin kawunsa, wanda shi ma mai maganin gargajiya ne shi ya ba shi kafin rasuwarsa.

Ya kara da cewa mutanen sa ne suka kai kararsa saboda yana yin tsafi kuma duk lokacin da yake dauke da kayan aikinsa idan ya taba mutum azzakarinsa ya kan bata.

 

 

Ya kara da cewa ‘yan sanda sun yi nasarar kama shi ne kawai saboda tsafinsa ya yi tafiya a lokacin da aka zo kama shi.

Ya kira tsare shi da aka yi keta doka, domin a fadar sa babu wata doka da ta yarda a kama masu maganin gargajiya. Sannan ya bukaci a sake shi ya tafi gida lami lafiya ba tare da bata lokaci ba.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like