An Kama Shugaban Ƙaramar Hukuma Da Kuma Wasu Mutane Da Ake Zarginsu Da Yuƙurin Kisan Sanata Dino Melaye


nigeria-police

Rundunar ƴan sandar Najeriya ta gabatar da shugaban ƙaramar hukumar Ijumu dake jihar Kogi Taofiq Isah da kuma wasu mutane gsu biyar kan zargin yunƙurin kisan Sanata Dino Melaye.

Mai magana da yawun rundunar CSP jimoh Moshood  ya bayyana haka yau Asabar a hedikwatar rundunar dake Abuja, yace an gano makamai da kuma motar ɗaukar marasa lafiya da akayi amfani da ita wajen yunƙurin kisan ɗan majalisar.

Yace bayan da wasu ƴan bindiga da ba’asan ko suwaye ba suka kaiwa ɗan majalisar dattawan hari  a gidansa dakeIyala a  ƙaramar hukumar Ijumu dake jihar Kogi, a ranar 15 ga watan Afirilu shekarar 2017 da misalin ƙarfe 12:30 na dare, babban sifetan ƴan sanda ya bada umarnin ayi cikakken bincike kan harin.

Bayan  shafe kwanaki goma ana gudanar da bincike ƴan sanda sun kama mutane shida da suke da hannu a yunƙurin kisan.

Yace babban wanda ake zargi Taofiq Isah, wanda ake zargi da kitsa kisan ɗan majalisar, ana zargin Isah da umartar wani Abdulmumini da akafi sani da Iron,wanda ba’asan inda yake ba  a yanzu, wanda a kace mai taimaka masa ne na musamman, kan ya nemo ragowar mutanen da suka kai harin.

Sauran waɗanda aka kama sun haɗa da Ade Obage,Abdullahi da akafi sani da Eko, Ahmad Ajayi,Micheal Bamidele da kuma wani tsohon sajan ɗin ƴan sanda Ede James.

Da yake amsa tambayoyin manema labarai shugaban ƙaramar hukumar ya musalta zargin da ake masa inda yace wata maƙarƙashiyace kawai don a ɓata masa suna.

You may also like