An Kama Wani Mai Faskare da Laifin Yi Wa Kananan Yara Fyade


 

 

‘Yan sandan jahar Niger sun kama wani mutum mai sana’ar faskare a bisa zargin da ake masa na yin lalata da kananan yara wadanda shekarunsu bai kai 15 ba.

Wannan ya biyo bayan gano mutumin da wata kungiyar kare hakkin yara ta yi. Mutumin mai suna Abdullahi mai faskare ya ja hankalin yaran guda biyu Maimuna da Saratu ‘yan kimanin shekaru 9 wadanda aka kawo su aikin aikatau garin Minna, zuwa dakinsa inda ya yi lalata da su, sannan ya baiwa daya daga cikinsu naira 20.

Abdullahi ya ci gaba da aikata wannan danyen aiki ba sau daya ba sau biyu ba, har ranar da dubun sa ta cika.

Shugabar kungiyar kare hakkin yaran, Barista Maryam Haruna Kolo ta ce wanda ake tuhumar ya yi amfani da kananan yara ‘yan kasa da shekaru 15 wanda hakan cin zarafin yara ne. Ta ce kungiyar ta kai yaran asibiti domin duba lafiyarsu, sannan kuma za su tabbatar cewa yaran sun koma makaranta.

Ta kuma ce da zarar ‘yan sanda sun kammala bincike za’a kare hakkin yaran a gaban kuliya.

Yanzu haka Abdullahi ya na tsare a ofishin ‘yan sanda na Tudun wada, Tunga da ke garin Minna a jahar ta Niger.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like