Duk da kisan ƴan Najeriya da akayi a kwanakin baya a ƙasar Indonesia kan safarar miyagun ƙwayoyi sai gashi hukumomi a filin jirgin saman Murtala Muhammad dake Lagos sun damƙe wani matashi na yunƙurin safarar hodar iblis samfurin Methamphetamine zuwa ƙasar ta Indonesia.
Matashin ɗan shekara 33 mai suna Lotachuku Umeme da yake ɗauke fasfo ɗin ƙasar Kodebuwa mai ɗauke da sunan Grou Bi Clauvis an kama shine lokacin da yake ƙoƙarin hawa jirgin kamfanin Qatar Airways zuwa Indonesia.
Bayan gwajin da akayi masa ya tabbatar ya haɗiye miyagun ƙwayoyi, Ƙunshi 89 na ƙwayar methemphetamine mai nauyin kilogiram 1.205 aka samu daga gurinsa, a sanarwar da hukumar yaƙi da sha da kuma fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa NDLEA ta fitar.
Indonesia dai na zartar da hukuncin kisa ga duk wanda aka samu da yunƙurin safarar miyagun ƙwayoyi zuwa ƙasar.
Ahmadu Garba shugaban hukumar ta NDLEA yace binciken farko da sukayi sun gano cewa mutumin ya fito ne daga jihar Anambra kuma sunansa na asaline shine Umeme Lotachuku Fabian.
A jawabin da yabayar Umeme yace anyi masa alƙawarin za a bashi $5000 don yakai ƙwayar ƙasar ta Indonesia.
Umeme ya ƙara da cewa shi kaɗai ne ɗa a gurin iyayensa, kuma yana so ya saka kuɗin da zai samu cikin harkokin kasuwancin sa, sannan yafara shirin yin aure.
Ya kuma ce bai san hukuncin kisa ake yankewa mai safarar ƙwaya a ƙasar ta Indonesia ba.
Hukumar ta NDLEA tace za a gurfanar dashi a gaban kotu bayan an kammala bincike.