Kungiyar sa ido kan harkokin tsaro a duniya watau International Crisis Group, ta ce wasu fiye da dubu 150 sun rasa muhallansu da kuma tilastawa wasu mutanen dubu 78 yin gudun hijira.

Kungiyar ta ce ko da yake hare haren da kungiyar ke kai wa sun fi kamari a lardin arewa mai nisa, matakan da gwamnati ta kaddamar na yaki da kungiyar suna yin nasara sai dai akwai bukatar kara kaimi da kuma hadin kai tsakanin kasar ta Kamaru da kasashe makwabtanta wajen yakin da Boko Haram. Abdullahi Tanko Bala ya tattauna da Hans De Marie Heungoup wani manazarci a kungiyar sa idon ta InternationalCrisis Group ga kuma rahoton da ya hada mana.
Kungiyar sa idon kan harkokin tsaro ta International Crisis Group a Kamaru ta ce ko da yake mahukuntan na Kamaru suna samun nasara a yakin da suke yi da Boko Haram musamman a lardin arewa mai nisa, har yanzu ba’a kawar da matsalolin da ke zama taki ga rikicin ba. Wadannan matsaloli a cewar Hans De Marie Heungoup na kungiyar ta ICG a Kamru sun hada da matsaloli na talauci abin da yace kungiyar ta Boko Haram ke amfani da wannan dama wajen jan ra’ayin matasa ta hanyar yi musu dan hasafi .

“Abin da yake a zahiri dai shine cewa kantar talauci a arewacin Kamaru ya bada damar shigar ‘yan Boko Haram tare da daukar mayaka a tsakanin al’umma musamman a yankunan kan iyaka kamar Fotokol da Kolo fata da sauran yankuna na kan iyakar.”
Ya ce idan aka yi lakari, za’a ga cewa Boko Haram, sannu a hankali ta shiga kasar Kamaru daga watan janairu na shekarar 2014 inda ta ke yin barazana ga hukumomi har ma da gargadin kasar kada ta sa kan ta a rikicin da kungiyar ke yi da Najeriya. Sai dai kuma bayan da kasar ta Kamaru ta zafafa kai farmaki kan kungiyar ta Boron Haram, kungiyar ta ce ta ja daga, kuma ta shiga yaki da kamarun ta hanyar kai hare hare ba kakkautawa.