Kame na ci gaba a Turkiya


 

Gwamnatin Erdogan na ci gaba da farautar mutanen da ake tuhuma da juyin mulkin da bai yi nasara ba inda jiya aka tsare gwamnoni uku da wasu ‘yan jarida tara.

A kasar Turkiya har yanzu ana ci gaba da kame mutanen dangane da juyin mulkin da bai yi nasara ba. Kamun baya-bayan nan shi ne wanda aka yi na tsare wasu ‘yan jarida tara, da wasu gwamnoni uku hade da wani babban jami’in ‘yan sanda, duk ana tuhurmarsu da hannu kan juyin mulkin. Dama dai tuni kotu a Istanbul, ta fidda sammacin kamo ‘yan jarida 35 bisa tuhumarsu da kusanci da sojojin da suka kitsa kifar da gwamnatin shugaba Erdogan, a ranar 15 ga watan jiya.

You may also like