Kamfanin Etisalat Na Dab Da Durkushe WaKamfanin sadarwa na wayar hannu ta Etisalat Nijeriya na dab da tattara ya nasu-ya nasu su bar Nijeriya bayan da babban kamfanin nan na kasar United Arab Emirates da ya sanya hannun jari a kamfanin wato Mubadala Development Company suka janye jarin da suka saka kuma suka fice suka bar kasar Nijeriya. 

Majiyarmu ta bayyana cewa shi ke da kaso 70 cikin 100 na jarin Etisalat inda EMTS da Bello Osagie ke jagoranta ke mallakar ragowar kaso 30 din da ya rage.

Tuni dai dama Mubadala ta sanar da Etisalat Nijeriya da hukumar kula da harkokin sadarwa ta kasar Nijeriya NCC bukatarta na ficewa daga Nijeriya.

Mun samu labarin cewa kamfanin Etisalat Nijeriya dai a baya-bayan nan ya fada matsalar tabarbarewar tattalin arziki tun lokacin da bankuna a ciki da wajen Nijeriya a karkashin jagoranci Zenith Bank suka matsa wa kamfanin ya biya bashin da ake binsa da ya kai dalar Amurka biliyan 1.72 daidai da Naira biliyan 541.8 da kamfanin Etisalat ya ci a shekarar 2015.

Etisalat ta ciwo bashin ne don ta inganta harkokin gudanarwarta dakarfafa layinta a fadin Nijeriya.

Gaza cika alkawarinta na biyan bashin a shekarar 2016 ya sanya bankunan da suka bata bashin a ciki da wajen Nijeriya suka hada kai a karkashin jagorancin Zenith Bank suka yi karar Etisalat ga Babban Bankin Nijeriya CBN da kuma Hukumar Kula Da Harkokin Sadarwa Ta Nijeriya NCC.

NCC ta sanya baki wajen shiga tsakanin bankunan da Etisalat Nijeriya wajen ganin cewa bankunan ba su karbe ikon Etisalat din ba. 

Inda aka sake zama a teburin sulhu aka fitar da sabon lokacin Etisalat za ta biya bashin.

You may also like