Kamfanin Etisalat Ya Janye Daga Nijeriya Rahotanni daga Abu Dhabi na hadaddiyar Daular Larabawa na cewa kamfanin Etisalat ya  janye samfurinsa daga Nijeriya.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya ruwaito cewar uwar kamfanin Etisalat dake birnin Abu Dhabi na hadaddiyar Daular Larabawa ya warware yarjejeniyar gudanarwa da ke tsakaninsa da reshensa na Nijeriya.

Wannan matakin ya biyo bayan gazawar da kokarin hukumar kula da kamfanonin sadarwar Nijeriya ta yi na ceto kamfanin daga durkushewa ta hanyar sake yarjejeniya kan bashin dala biliyan 1.2 da bankuna ke bin kamfanin.

You may also like