Biyo bayan kaddamar da fasahar laluben yanar gizo ta 4G LTE mai sauri, kamfanin sadarwa na Globacom yace ya fadada wannan fasaha har zuwa garuruwa 33 a fadin Najeriya.
A baya bayan nan ne kamfanin sadarwar ya samar da wannan fasaha a wasu jihohi har 12 wadanda uku daga cikinsu suka hada da jihohin Arewa, wato babban birnin Tarayya Abuja da Jos ta jihar Plateau da kuma Yola ta jihar Adamawa.
A lokacin kaddamar da wannan fasaha ta 4G LTE, kamfanin Globacom yace wannan zai taimaka masa wajen karfafa alkawarinsa na ganin cewa ya fadada fasahar zuwa sauran birane a fadin Najeriya.
4G LTE fasaha ce da wayoyin zamani smart phones a turance ke amfani da ita wajen samun network mai karfi da sauri.
3G LTE itace fasahar da ake amfani da ita a Najeriya kafin fitowar 4G LTE.
Cikin manyan abubuwan da duk masu layin Globacom da ke da fasahar 4G LTE zasu mora kyauta, sune milyoyin wakoki da hotunan bidiyo da finafinai.
A baya Bayan nan ne dai kamfanin MTN ya fara amfani da Fasahar 4G LTE a mafi yawanci garuruwan Najeriya , wanda suka hada da jihohin arewa da yawa, hakan ya samo asali ne tun bayan da kamfanin na MTN ya siji Manhakar Tsohon Kamfanin sadarwar nan Na VisaFone.