Kamfanin Google Na Yaki Da Satar Basirar Mawaka


3042974-poster-1280-android-google-work-phone-incentive

 

 

Kamfanin google, ya bayyanar da yunkurin shi na kokarin kare hakokin mawaka, wanda hakan yasa ya kashen makudan kudade da suka kai kimanin dallar Amurka, billiyan biyu $2B. Wadannan kudaden an kashe sune wajen hadin gwiwa da kamfanin youtube, don karema mutane hakkin su na abubuwan da suke sakawa a shafufukan yanar gizo.

Yunkurin kamfanin shine, a dakile hanyoyin satar basira, mawaka da dama na ganin cewar kamfanin shine yake bada damar mutane suna satar wakokin wasu. Saboda yadda suke saka labarai da dimidimin su. Duk dai da yunkurin kamfanin na samar da lambar gabatarwa a shekarar 2014, ga kowane mai saka waka a shafufukan yanargizo abun dai bai samu nasara ba.

Yanzu haka dai kamfanin na google sun samarwa samada mutane milliyan hamsin, da suke da lambar mallakan wani abu da suka saka a yanar gizo, suna kuma cigaba da yunkurin kara samar da wannan lambar ga sauran mutane. Domin tahaka ne kawai za’a iya magance satar waka ko wata basira ta mutane. Sun kara kira ga mutane da su guji satar basirar wasu, wanda idan suka samu mutun da wannan halin zasu rufe account din shi da gaggawa.

 

 

 

 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like