Kamfanin Jaridar Business Day Ya Karrama Gwamnan Jihar NejaA taron neman masu saka jari da gwamnatin Neja ta shirya a karkashin jagorancin gwamnan jihar, Abubakar Sani Bello, kamfanin jaridar Kasuwanci da ake kira a turance, “Business Day” ya karrama gwamnan bisa zama zakaran gwamnoni da ya yi a bangaren karfafa matasa da mata.

Da ake karrama gwamnan a dab da rufe taron da aka dauki kwana biyu ana gudanarwa a Minna, babban editan kamfanin ya bayyana cewa, kamfanin ta dubi cancantan gwamnan ne, bisa kokarinsa a bangaren karfafa mata da matasa, duba da matakin fadiwan tattalin arziki da ake ciki.

A jawabinsa na rufe taron, gwamnan Abubakar Sani Bello, ya mika godiyarsa ga dukkan wanda suka halaraci taron.

Gwamnan ya kara da cewa, ma’aikatan da aka shirya taron karkashinta za ta tattara dukkan bayanan da aka tattauna a kai sannan ta fitar da tsari da dabarun da za a yi aiki da shi ga abubuan da aka tattauna a kai.

Wadanda suka halarci rufe taron sun hada  babban dan kasuwa kuma tsohon gwamnan jihar Kano a lokacin mulkin soja, Kanal Sani Bello mai ritaya, karamar ministar kasafi Hajiya Zainab Ahmed, tsohuwar ministan harkokin Neja Dalta Hajiya Zainab Kuchi.

Saura kuma sun hada da ‘yan kasuwa masu saka jari, kwamishinoni, wakilin gwamnan jahar Kwara da dai sauransu.

Bude taron ya samu halarta makadashin shugaban kasa Farfesa Yemi Osibanjo, Tsofaffin shuwagabannin kasa,  Janar Olusegun Obasanjo, Janar Abdulsalam Abubakar da dai sauran manyan ‘yan siyasa da ‘yan kasuwa. 

You may also like