Kamfanin Jirgin Sama na Arik Ya Rufe Aiki


arik-air2

 

Daruruwan matafiya ne suka kasa komawa garuruwansu bayan da jirgin kamfanin Arik ya gaza tashi a safiyar jiya Talata.

Tun safiyar jiyan, babu daya daga ciki jiragen na kamfanin Arik wanda ya tashi zuwa wani masaukinsu a yammacin Afirka.

Wannan ya biyo bayan dumbin bashin da ‘yan kasuwan mai ke bin kamfanin jirgin na man jirgi da suka saba samar da su. Bayan haka, kamfanin insuran jirgin da ke nahiyar turai ya janye insura akan su, al’amarin da ya sanya jirgin ya rufe aiki gaba daya.

Wata majiya ta bayyana cewa ana bin kamfanin na Arik akalla naira biliyan 3, a domi haka ne ‘yan kasuwan man su ka janye samar da man jirgi  kamar yadda suka saba ga kamfanin.

Arik dai ya zama kamfanin jirgi na 3 kenan da ya rufe ayyuka a cikin sati ukun nan da suka gabata, ya bi sahun kamfanin Aero da First Nation.

You may also like