Kamfanin Man NNPC Zai Fara Saida Wa Dillalan Man IPMAN Mai Kai TsayeGa dukkan alamu karancin man fetur da hauhawar farashin mai da ake fuskanta a fadin kasar zai yi sauki nan da ‘yan kwanaki bayan wata yarjejeniya da kungiyar dillalan man fetur ta kasa wato IPMAN ta cimma da kamfanin man fetur na kasa. Mataimakin shugaban kungiyar IPMAN Abubakar Maigandi Dakingari, shi ne ya tabbatar wa Muryar Amurka da haka a wata hira ta musamman.

Maigandi ya ce kungiyar ta zauna da kamfanin man fetur na kasa inda suka cimma wannan yarjejeniya, to sai dai ya ce kullum haka kamfanin ya ke gaya masu cewa za a kawo masu dauki, amma sau tarin yawa ba a cika masu alkawalin.

Maigandi ya kuma ce kungiyar IPMAN ita ce take da kashi tamanin cikin dari na wuraren sayar da mai, saboda haka wannan mataki zai taimaka wa talaka da kuma gwamnati. Maigandi ya ce idan aka samu sabani a wannan yarjejeniyar, to dole ne dillalan man fetur su kara kudi akan ka’idar da gwamnati ta bayar na sayar da lita daya akan Naira 195.

Tallafin Mai A Najeriya Ya Haura Dala Biliyan 1 A Watan Agusta Yayin Da Take Kara Samar Da Man Fetur

Tallafin Mai A Najeriya Ya Haura Dala Biliyan 1 A Watan Agusta Yayin Da Take Kara Samar Da Man Fetur

Shin ko wannan mataki yana da nasaba da kwamitin mutum 14 da shugaba Mohammadu Buhari ya ke jagoranta?

Tsohon mataimakin shugaban kungiyar ma’aikatan man fetur ta kasa Komred Isa Tijjani, ya yi tsokacin cewa kafa wani kwamiti bayan shugaba Buhari ya kwashe shekaru da dama a matsayin Ministan man fetur a kasar ma abin mamaki ne, domin har yanzu ana nan ne kamar a wuri daya ake tsaye, babu gaba babu baya.

Ghana Zata Iya Fuskantan Matsalan Karancin Mai Sakamakon Matakin Bankin Kasar Na Rage Yawan Dalan Amurka Da Take Fitarwa

Ghana Zata Iya Fuskantan Matsalan Karancin Mai Sakamakon Matakin Bankin Kasar Na Rage Yawan Dalan Amurka Da Take Fitarwa

Isa ya ce bai ga amfanin wani Kwamiti ba, sannan kwan-gaba-kwan-baya da harkar fetur ke yi kowa ya san murdiya da sama da fadi kawai ake yi da dukiyar kasa. Ya kamata a yi wa bangaren man fetur garambawul.

Shi kuwa shugaban Kungiyar fafutukar kwato wa talaka yanci Abubakar Abdulsalam, ya ce ko a wannan kokari da kamfanin NNPC ya yi dole ne shugaban kasa ya sa ido tunda za a ba kungiyar dillalan man fetur kai tsaye, domin akwai baragurbi a cikin su.

ABUJA: NNPC

ABUJA: NNPC

Abdulsalam ya kuma ce sune suke cuwa-cuwa da man, suna ba ‘yan bumburutu domin su sayar da shi a farashi mai tsada, wasu kuma suna fasakwaurin man zuwa kasashen ketare da ke makwabtaka da Najeriya.

Ya kara da cewa idan ba a dauki irin wannan mataki ba, ba za a ga karshen karancin man fetur da kuma layukan motoci a gidajen mai ba.

Abin jira a gani shi ne idan wannan yarjejeniya tsakanin kamfanin NNPC da kungiyar dillalan man fetur zata dore har zuwa watan Yuni da Gwamnati ta ce zata cire hannunta a tallafin man fetur a kasar.

Saurari rahoton Medina Dauda Daga Abuja.Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like