Kamfanin MTN A Nigeria Ta Fitarda Kudade Masu Yawa Daga Kasar Ta Barauniyar Hanya


4bk523ee0d56ab70k1_800c450

 

Wani sanato daga mazabar jihar Osun ta tsakiya ya bayyanawa majalisar dattawan Nigeria kan cewa Kamfanin MTN ta wayar tafi da gidanka ya fitar da makodan kudade daga kasar ta barauniyar hanya.

Kamfanin dillancin labaran Reuters ya nakalto Senator Olusola Adeyeye yana fadar haka a zauren majalisar dattawan Nigeria a yau Alhamis ya kuma kara da cewa dole ne majalisar ta gudanar da binciken da ya dace don gano gaskin abinda ya faru.

Sanaton yana magana ne a dai dai lokacinda majalisar take fara bincike kan zargin cewa kamfanin na MTN mallakin kasar Africa ta Kudu ta fitar da kudade wadanda yawansu ya kai dalar Amurca billiyon 14 ba tare da bin ka’idojin kasar na fitar da kudade ba.

Kamfanin MTN dai ta musanta zargin ta kuma bayyana cewa zata kare kanta a duk lokacinda bukatar hakan ta taso.

Har’ila yau ana zargin ministan masana’antu kasuwanci da kuma zuba jari Mr Okechukwu Enelamah da hada kai da kamfanin na MTN wajen fitar da wadan nan makudan kudade ba tare da bin ka’adojin fitar da su daga kasar ba. Ministan ya rubutawa majalisar dattawan Nigeria wasika inda yake musanta zargin. Ana saran majalisar zata ci gaba da tattauna batun a cikin yan makonni masu zuwa.

You may also like