Kamfanin NNPC ya Shigo Da Man Jirgin Sama Kimanin Lita Miliyan 38Biyo bayan karancin man fetur na jiragen sama da ake fama da shi a kasar nan, kamfanin man fetur na kasa wato NNPC ya shigo da lita miliyan 38 da ‘yan kai domin shawo matsalar da ta addabi zirga-zirgan jirage cikin kasar.
Rahotani sun nuna wasu jiragen da kan shiga Nijeriya sai sun biya ta kasar Ghana su sha mai kafin su cigaba da tafiyarsu.
Jami’in labaru na kamfanin NNPC shi ya bayyana matakin da kamfanin ya dauka domin rage kalubalen da ake fuskanta a daidai lokacin da ake zirga zirgan karshen shekara da ya hada da bikin kirsimati da sabuwar shekara.
Yayin da yake jajinta kalubalen da kan haddasa cunkoso a filayen jirage da ma soke tashin jiragen na cikin gida da na ketare ministan zirga zirgan jiragen saman Nijeriya Hadi Sirika ya ce damuwar ta wucin gadi ce. Yace sun nunawa kamfanin NNPC mahimmancin fara yin man a Najeriya domin da can ana yi a Kaduna da Fatakwal.Kamfanin yayi alkawarin zasu fara yi kwana kwanan nan. 
Bacin hakan sun je babban bankin Nijeriya da ma’akatar kudi cewa ya kamata a ba ma’aikatar jiragen sama mahimmanci a samo dalar Amurka domin a shigo da man. Bayan wadannan Hadi Sirika ya ce sun lallashi masu hannu da shuni kaman kamfanin MRS da Sahara suka rokesu su shigo da man domin a samu maslaha.

You may also like