Kamfanin NNPC ya yi barazanar hukunta dillalai dake boye mai


Kamfani Mai na Ƙasa NNPC yayi barazanar hukunta duk wani dillalin man fetur da aka samu da boye mai.

Kamfanin ya kuma shawarci masu ababen hawa da su guji siyan man da yawa boyewa saboda fargabar fuskantar karancinsa  domin kamfanin ya samar da man wadatacce da zai ishi kowa.

 Karancin man ya kara ta’azzara bayan da kungiyar manyan ma’aikatan mai da iskar gas PENGASSAN suka fara wani yajin aiki a ranar Litinin.

Duk da kungiyar ta janye yajin aikin da ta shiga har yanzu ana cigaba da fuskantar karancin man a gidaje mai dake faɗin kasarnan.

Kamfanin ya gargadi dillalai da kada su boye man domin kuwa jami’an tsaro suna aiki tukuru don ganin an lalubo masu kunnen koshi domin hukunta su kamar yadda doka ta tanada.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like