Kamfanin NNPC yace babu shirin karin farashin kudin mai 


Kamfanin mai na ƙasa NNPC yace babu shirin karin farashin man fetur duka kan yadda ake bayarwa kan sari da kuma yadda gidajen man fetur ke siyarwa.

Kamfanin ya  bayyana haka ranar Litinin cikin wata sanarwa da yafitar  kan jita-jitar da ake yadawa cewa akwai yiyuwar za a kara farashin kuɗin mai.

A wata sanarwa da  Ndu Ughamadu manaja mai kula da ɓangaren hulɗa da jama’a na kamfanin yafitar tace har yanzu farashin a defo yananan akan ₦133 kowacce lita yayin da farashin a gidajen mai bai canza ba daga ₦143 da kuma ₦145.

Ya kuma ce kamfanin yana ajiye da mai domin rabawa ba tare da an samu tsaiko ba.

 Yayin da yake  kira da ayi watsi da jita-jitar kamfanin na NNPC yace yana da goyon bayan dukkanin masu ruwa da tsaki an bangaren samar da mai da suka hada da kungiyar dillalan mai da kuma ta ma’aikata dake aiki a fannin mai don ganin cewa ba a samu matsalar mai ba yayin bukukuwan karshen shekara.

Kamfanin ya kuma yi kira ga masu motoci da su kaucewa dabi’ar nan ta sayan mai a jarakuna suna ajiyewa a gidajensu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like