Kamfanin NNPC Zai Cigaba Da Aikin Tono Mai A Jihar Borno Shugaban kamfanin mai na kasa NNPC,Maikanti Baru yace nan gaba cikin makonni shida kamfanin zai dawo da aikin hakar mai da yakeyi a yankin tafkin Chadji. 

 Da yake magana a ranar talata lokacin da yakaiwa gwamnan jihar Borno Kashim Shetima  ziyara, Baru wanda ya samu wakilcin Saidu Muhammad, shugaban bangaren kula da iskar gas da kuma wutar lantarki, yace wannan ya zama dole domin alkinta albarkatun mai da iskar gas da kasarnan take dasu,dan bunkasa tattalin arzikin kasa. 
Yace kamfanin zai tura tawagar kwararru zuwa yankin na tafkin Chadji tare da kayan aiki na zamani domin cigaba da aikin hako mai a yankin
Shugaban ya kuma yabawa gwamnatin jihar a kokarin da take na sake ginawa da kuma tsugunar da al’umomin da rikicin ya raba da gidajensu. 

“Munzo Borno ne domin nuna cikakken goyon bayan mu ga gwamnatin jihar Borno a kan namijin kokarin da take na sake tsugunar da al’umomin da rikici ya shafa,”Baru yace. 

” Saboda haka NNPC, na duba inda yakamata ace ta bada nata tallafin,saboda girman barnar da akayi abin damuwa ne matuka.

“kuma munzo jihar ne domin mu sanar dakai cewa nan da sati 6 masu zuwa zamu turo da tawagar kwararru zuwa nan Maiduguri,domin cigaba da aikin tono mai a yankin tafkin Chadji.”

A bangarensa gwamna shettima, yace gwamnatinsa zata hada hannu da NNPC wajen aikin hako man. 

Yace hakan zai samar da kudaden shiga da kuma guraben aiyukanyi masu yawan gaske.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like