Kamfanin NNPC Zai Fara Haƙo Mai A Jihar Bauchi


Shirye-shiryen fara hako mai a jihar Bauchi ya yi nisa, inda nan ba da jimawa ba hukumar NNPC za ta fara hako mai a jihar.

Babban manajan kamfanin NNPC Maikanti Kachalla Baru ne ya bayyana hakan a ofishinsa a yayin ziyarar da gwamnan Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya kai masa jiya a ofishinsa da ke Hedikwatar hukumar a Abuja.

Gwamnan Bauchi ya ziyarci babban manajan NNPC ne don jijjina masa bisa yadda hukumar ke aiki tukuru a jihar ta Bauchi.

Da ya ke jawabi, Maikanti Baru ya bayyana wa gwamnan cewa shirye-shiryensu na fara aikin tono mai ya kai matakin karshe, inda ya ce rijiyoyin mai 5 ne za a fara tonowa karamar hukumar Alkaleri.

Ya ce NNPC, za ta yi amfani da ingantattun kayan aiki na zamani domin fara wannan aikin a waddanan wurare kamar yadda suka samu umarni daga gwamnatin tarayya.

Gwamnan jihar Muhammad Abdullahi Abubakar ya bayyana shirinsa na ba da dukkan gudunmawarsa ga hukumar NNPC domin fara wannan aikin.

Daga karshe gwamnan ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba jihar Bauchi za ta shiga sahun jihohi da ke hako mai a Najeriya.

Mun samu wannan sanarwar ne daga mai taimakawa gwamnan na musamman dagane da harkokin sadarwa Shamsuddeen Lukman .

You may also like