Kamfanin NNPC zai gina tashar samar da wutar lantarki a Abuja,Kaduna da kuma  Kano


Kamfanin mai na ƙasa NNPC ya ce zai gina tashar samar da wutar lantarki mai karfin 4600mw  a biranen Abuja, Kano da kuma Kaduna.

A wata sanarwa a Abuja da mai magana da yawun kamfanin Mista Ndu Ughamadu yafitar, ya ce za ayi hakane ta hanyar kwangilar  da aka  bayar kwanannan ta shinfida bututun iskar gas daga Ajaokuta-Abuja-Kaduna-Kano wanda ake wa lakabi da Layin Bututun AKK.

A cewar sanarwar, aikin shinfida bututun na AKK ya fara haifar da amfani da wurwuri idan aka yi duba da ƙoƙarin da NNPC keyi na gina tashoshin samar da hasken wutar lantarki da za su rika samar  da jumullar wutar lantarki mai karfin  4550mw a Abuja, Kaduna da Kano.

Ughamadu ya jiyo shugaban kamfanin na NNPC Maikanti Baru na cewa kamfanin tare da haɗin gwiwar masu zuba jari za su gina tashoshin samar da wutar lantarki domin tallafawa yinkurin gwamnatin tarayya na samar da wutar lantarki mai dorewa.

You may also like