Kamfanin Sarrafa Tumatur na Dangote wanda ke Kadawa a Karamar Hukumar Kura a jihar Kano zai dawo aiki a watan Fabrairun 2017. Kamfanin wanda ya fara aiki a watan Fabrairun bara ya tsayar da aiyukansa ne sakamakon rashin kayan sarrafawa.
Kamfanin dillancin Labarai, NAN ya rawaito Babban Manajan kamfanin, Alhaji Abdulkadir Kaita, yana cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen dawowa aiki. Kaita ya ce kamfanin ya rufe ne saboda annobar tsutsar tumatur da ta kassara gonakai a jihohi biyar da suke sayar musu da kaya.
Abdulkadir yace dukkan ma’aikatansu suna nan daram kuma suna ci gaba da biyansu albashi a kowanne wata kuma akwai yiwuwar zasu ɗebi sabbin ma’aikata saboda ƙara inganta aiyukansu.
Kamfanin wanda yafi kowanne girma a Nahiyar Afrika, yana da ƙarfin sarrafa ton 1,200 ko kuma kwatankwacin mota 40 na tumatur a kowacce rana.