Kanawa Sunyi Taron Nuna Har Yanzu Fa Shugaba Buhari Ne Gwarzon SuDandazon magoya bayan shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Alhamis sun gudanar da addu’o’i na musamman ga shugaban kasan a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata cikin birnin Kano don nuna farin cikin su da dawowarsa daga jinya da kuma fatan Allah ya kara masa lafiya.

Daga bisani dandanzon jama’an karkashin jagorancin hadimin shugaba Buhari kan kafafun sadarwa, wato Sha’aban Ibrahim Sharada sun dunguma zuwa fadar gwamnatin Kano, inda gwamna Ganduje ya tarbe su.

Gwamnan ya nuna farin cikinsa game da yadda ya ga dandanzon magoyan bayan shugaban kasan, wanda a cewarsa hakan ya nuna cewa har yanzu al’ummar jihar Kano na tare da shugaba Buhari dari bisa dari.

You may also like