KANNYWOOD: Jaruman Arewa Sun Kwashi Garabasa A Gasar ‘City People Magazine’


 

 

Shahararren jarumi, mawaki kuma darakta Yakubu Muhummad ya lashe gasar gwarzon jarumi ta bana da Mujallar City People Entertainment ta garin Legas ke shiryawa. A bangaren mata kuma Nafisa Abdullahi ce ta zamo gwarzuwa tsakanin takwarorinta. Yayin da Rahma Sadau ta lashe kyautar jarumar da ta fi haskawa a bana (Face of Kannywood) Mujallar City people tana shirya wannan gagarumar gasa duk shekara domin karrama wadanda suka taka rawa a farfajiyar finafinan Nijeriya ciki har da bangaren Arewacin kasar watau Kannywood.

Da yake bayyana farin cikinsa, Yakubu Muhammad ya ce bai taba tsammanin zai lashe gasar ba, kwatsam sai ya ji sunanansa ya fito a matsayin gwarzo duk da bai samu halartar wajen ba sakamakon wasu ayyuka da suka sha masa kai.

Ita ma jaruma Nafisa ba ta halarci taron ba saboda wasu dalili, sai dai ta yi godiya matuka ga wadanda suke shirya wannan gasa bisa duba cancantar da suka yi na zabarta a matsayin gwarzuwar jaruma.

Darakta Hassan Giggs shi ne ya lashe gwarzon mai bada umarni, yayin da Alhaji Sani Sule Katsina (Real Love) ya lashe kyautar gwarzon mai shirya finafinai. Ga jerin yadda gasar ta bana:

Gwarzon Jarumi: Yakubu Muhammad

Gwarzuwar Jaruma: Nafisa Abdullahikyauta

Gwarzon Darakta: Hassan Giggs

Gwarzon Fim: Gwaska

Jaruma Da Ta Fi Hasakawa: Rahma Sadau

Gwarzon Furodusa: Alhaji Sani Sule Katsina (Real Lobe)

Gwarzuwar Jaruma Mai Tasowa: Hanan Bashir.

You may also like