Kano- ‘Yan Sanda Sun Samu Nasarar Cafke Masu Garkuwa Da Mutane*An Ceto Mutane 12 Daga Wurinsu

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ta yi nasarar cafke wasu masu garkuwa da mutane har su goma sha daya tare kuma da ceto mutane sha biyu daga wurinsu.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Rabi’u Yusuf ya bayyana cewa an gano bindiga da harsashai a wurin wadanda ake zargin.
Kwamishinan ya kara da cewa masu garkuwan suna gudanar da ayyukan su ne a yankin Dajin Falgore amma a yayin farautar da jami’nsu suka fita sun yi nasara akansu.
Sauran kayan da aka gano a wajen su sun hada da tabar wiwi, kayan abinci da na sha da kuma sauran kayan amfanin cikin gida.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like