Karamar Hukumar Chanchaga Ta Fara Zakulo Ma’aikatan Boge


 

 

 

Kansila mai wakiltan mazabar Makera da cikin karamar hukumar Chanchaga, Hon. Ibrahim Adamu ya ce gwamnatinsu ta kafa kwamitin da zai tantance ma’aikatan karamar hukumar.

A cewarsa hakan ya biyo bayan rade-radin yawaitan ma’aikatan boge a karamar hukumar wanda tantancewar ce kawai za ta banbance ma’aikatan kwarai da na boge.

“Yanzu haka bayan ba ni matsayin kansila mai kula da sashen ilimi na karamar hukumata a yawon da na yi don sanin ainihin adadin makarantun da mu ke da su, na gano makarantu guda 31 amma kuma na hango akwai wani boyayyen abu a baya kan haka. Na mika rahato ga shugaban karamar hukuma kuma an sanya kwamiti dan bincikar abin da na hango, amma dai maganar ma’aikatan boge kam akwai su. Amma adadin su ne ba zan fadi ba sai kwamitin sun kammala aikinsu.

“Maganar malaman makaranta kuwa da ake korafi a kan ba a biya su ba, da zaran an kammala wannan binciken, nan ba da jimawa ba kowa zai ga albashinsu.

Dangane da adadin makarantun da aka ce an gano na boge kuwa, muna jiran rahoton kwamitin da aka kafa su yi bincike a kai kuma da zaran sun kammala za mu sanar da jama’a. Maigirma shugaban karamar hukumarmu, Alhaji Yusuf Inuwa Fuka ya zo da sabon tsarin da zai zama karbabbe ga kowa, dan haka duk abin da muke yi muna yinsa ne a kan ka’ida, bayan nada mu a matsayin shugabannin hukumomin gwamnati da suka shafi karamar hukuma, a duk lokacin da aka kawo rahoto sai an kafa wani kwamitin musamman dan yin bincike tare da tabbatar da korafin da aka kawo wa hukumar zartaswa ta karamar hukuma, wannan na nufin samar da ingantaccen gwamnatin da za ta dora jama’a a kan turba.” In ji shi.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like