Karancin Fetur: Tankokin Mai 4,501 Ne Suka Ɓace – NNPC Shugaban Kamfanin Mai na Kasa ( NNPC), Maikanti Baru ya tabbatar da cewa kimanin tankoki makare da man fetur har 4,501 ne wasu dillalan mai suka tsallaka da su zuwa kasashen da ke makwaftaka da Nijeriya.

Ya ce, wannan daga cikin abubuwa da suka janyo har yanzu ake fama da matsalar man fetur inda ya kuma nuna cewa wasu dillalan man sun boye man a bisa tunanin gwamnati za ta kara kudin fetur.

You may also like