Karar Fashewar Wasu Abubuwa Har Sau 6 Ta Ratsa Birnin Maiduguri A Daren Jiya 


Hoto:The cable

Wata karar fashewar wani abu mai karfi ta ratsa birnin Maiduguri a daren jiya Talata.

Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa anji karar fashewar wasu abubuwa har sau 6 tsakanin karfe  10:45 zuwa 11:00 na dare. 

An tayar da abubuwan fashewar hudu a lokaci daya yayin da guda biyu aka tayar dasu bayan mintuna 15 da fashewar na farko.

 Amma ba kamar na farko ba wannan karar ta biyu mai karfin gaske ce da har takai ga motsa rufin gidajen wasu mutane.

Baza a iya tantance wurin da fashewar ta afku ba domin yinkurin da akayi najin tabakin hukumomin tsaro a jihar yaci tura domin masu magana da yawun hukumomin tsaro a birnin sun ki yarda su ce komai a kan lamarin. 

Sai dai wata majiyar tsaro ta tabbatar da cewa  Sojoji ne suka harba bindigar Atilare kan wani jerin gwanon motoci na yan kungiyar Boko Haram dake shirin kai hari birnin.

 

You may also like