Karatu kyauta ya zama dole a jihar Kaduna


Nasir-elrufai-2
Gwamnan Jihar Kaduna Mallam Nasir El-Rufai

 

 

Gwamnatin jihar Kaduna ta yanke shawarar mai da ilimin boko tillas na matakin firamari a kowace karamar hukuma jihar Kaduna guda ashirin da uku(24) a watan gobe.

Comisionan ilimin jihar ya bayan wa marubuta labarai hakan tare da cewa ilimin bokon firamarin zai zama doka a jihar baki daya a watan jibi(satumba).ya cigaba da cewa gwamnatin jihar ta sa dukan ne dun a sami ingantaccen ilimi a jihar ta Kaduna baki daya kuma tayi alkawarin hukunta duk iyayen da suka ki tura yayaensu makaranta.ta kuma kara da cewa duk yaran da  aka kama yana bara  za a dauki hukunci mai tsauri akan iyayan yaran.gwamnatin jihar tace za tasa duk wani almajiri a makaranta ta samani.

Comisionan ya kara da cewa gwamnatin ta fida kudi kimamin billian biyu da dugo biyu(N2.2 billion) na biyan sababin malamai dubu daya da dari biyu(1200) da aka dauka aikin.

 

 

You may also like