
Asalin hoton, GUINNESS WORLD RECORDS
Bobi ya karya tarihin da ake da shi a hukumar Guinness World Record, shi ne kare da ya fi dadewa a duniya
Wani kare a ƙasar Portugal ya zama wanda ya fi ko wanne kare shekaru a tarihin duniya, ya karta tarihin da aka shafe sama da shekara dari da kafawa in ji – Guinness World Records.
Bobi na cikin jinsin karnukan Rafeiro do Alentejo – da a rayuwa ba sa wuce shekara 12 zuwa 14.
Karen da a baya yake riƙe da wannan tarihi shi ne Bluey da ke Australia, wanda ya mutu a 1939 yana da shekaru 29 da wata biyar a raye.
Ranar 1 gawatan Fabirairu Bobi ya cika shekara 30 da kwana 226, kuma yana yin abin duk da ake so a wannan shekarun nasa.
An tabbatar da shekarun nasa ne ta hannun gwamnatin Portugal ƙarƙashin kulawar Hukumar Kula da Dabbobi ta ƙasar, kamar yadda Guinness World Records ta bayyana.
Ya na zaune da iyalan Costa a ƙayen Conqueiros a duk tsayin rayuwarsa, da suke zaune a gaɓar tekun Portugal, kuma yana da ‘yan uwa uku da mahaifiyarsa ta haifa.
Leonel Costa, wanda shekararsa takwas a lokacin, yace mahaifansa na da dabbobin da suke kiwo da dama, don haka suka yasar da wasu da yawa sai dai Bobi ya tsallake rijiya da baya.
Asalin hoton, GUINNESS WORLD RECORDS
A cewar Costa sirrin daɗewar Bobi ya samu yanayi mai kyau ne
Leonel da ɗan uwansa sun riƙa ɓoye Bobi suna ci gaba da kiwonsa, har sai lokacin da ya zama wani ɓangare na gidansu, wanda yake ba shi abinci irin wanda suke ci.
“Tsakanin abincin gwangwani na dabbobi da nama, Bobi bai fiye damuwa ya ci ko ɗaya ba, ya fi damuwa ya ci irin abin da muke ci, in ji Mista Costa, wanda ko da yaushe yake neman abincinsa cikin ruwa.
Bayan wata rashin lafiya da ya yi a 2018 har aka kwantar da shi a asibiti saboda gaza numfashi da ya yi, Mista Costa ya ce kare na rayuwa ne cikin kwanciyar hankali, kuma sirrin tsayin rayuwarsa shi ne “nutsuwa da samun muhallin da ke cike da zaman lafiya” da yake rayuwa cikinsa.
Kuma kamar gado ya yi daga wajen mahaifiyarsa, mahaifiyar Bobi sai da ta yi shekara 18 a raye.
Amma duk da haka, lokaci na neman cimma Bobi, domin yanzu yana da matsalar ƙafa da kuma gani.
Costa ya ce Bobi shi ne “na ƙarshe a tsarin dabbobin” a gidanmu kuma ya ce “shi ɗin na daban ne.”
Naɗin da aka yi wa Bobi na karen da ya fi daɗewa a duniya na zuwa ne mako biyu bayan Guinness World Records ta naɗa wani kare Spike the Chihuahua, mafi daɗewa a raye wanda ya kwashe shekara 23 a raye.
Amma bayan nan sai kungiyar ta sauya tarihin ta sanar da Bobi a matsayin karen da ya fi daɗewa a duniya.