Karfin Wutar Lantarkin Nijeriya Ya Karu Da Kusan Megawatts 500 a Mako Guda


wutar-lantarki

 

Kamfanin rarraba wutan lantarki na Nijeriya ya bayyana cewa adadin karfin wutar da ake samarwa da rabawa a fadin kasar ya karu daga megawatts 3,810 a ranar Alhamis, 8 ga watan nan zuwa megawatts 4,285.90 a yau Juma’a 16 ga watan Satumban 2016.

Kamfanin dillacin labarai ta Nijeriya NAN ta rawaito cewa Ma’aikatar samar da wutan lantarki ta kasa ce ta bayyana wannan labari a shafinta na yanar gizo a yau Juma’a.

Hukumar ta rubuta a shafinta, “A yau, Juma’a kamfanin samar da wutan lantarki ta rarrabawa kamfaninnikan rarraba wutan lantarki 11 da kasar ke da su karfin wuta megawatts 4,285.90.

Wutar lantarki ta samu a Nijeriya a ‘yan kwanakin nan sakamakon dagawar da karfin wutar ta yi daga megawatts 2, 983 zuwa megawatts 4,000 a cikin watanni 2.

Shugaban kula da samar da daidaiton wutar lantarki ta kasa (NERC), Dakta Anthony Akah ya bayyana cewa duk da wadatar da wutar lantarki ta yi a Nijeriya wasu da dama ba sa biyan kudin wuta akan kari sakamakon rashin yin amfani da mita da ba sa yi.

Dakta Akah ya bayyana cewa sama da gidaje miliyan 4 ne a fadin kasar nan ke amfani da wutar lantarki ba tare da mita ba.

Dakta Akah ya ce hukumar tasa za ta hukunta duk wani kamfanin rarraba wutar lantarki da ba ta sanya mita ga kowane gida da ta ke baiwa wuta ba saboda sai da mitar ne kadai hukumar za ta iya tabbatar da samar da wutar lantarki akan kari.

You may also like