Tsoffi da daraktocin hukumar NNPC na yanzu sun bayyana yadda ci gaba da sayar da man faetur a kan naira N145 ka iya kawo durkushewar hukumar.
Sun bayyana haka ne a wani taron kwana daya da suka yi da ministan man fetur Dr Ibe Kachikwu a garin Abuja.
Sun bayyana cewa farashin baya tafiya daidai da karin da ake samu a abubuwan da ke kayyade farashin man fetur din da kuma faduwar darajar Naira. Domin kuwa yayin da aka tsaida farashin akan naira 145, kudaden da suke kashewa na ci gaba da hauhawa.
Wannan al’amari ya kara tabbatar da gaskiyar wani rahoto da jaridar PUNCH ta wallafa a ranar 7 ga watan Ogusta da ke nuna cewa ‘yan kasuwar man sun ce farashin man fetur din na gaskiya shine 151.87
Daraktocin sun kuma ce suna fafutika ne kawai su ga sun tsayar da farashin nasu a kan naira 145, kuma idan haka ya ci gaba, hukumar za ta iya durkushewa.
Sai dai shugaban hukumar kwadago ta kasa Dr. Peter Ozo-Esun ya bayyana cewa ‘yan Nijeriya ba za su iya yarda da wani kari na farashin mai ba
cc: alummata