Karkashin gwamnatin Jonathan Boko Haram suna shiga Abuja a lokacin da suka ga dama – Kai Muhammad


Lai Muhammad ministan yada labarai da al’adu ya ce shekaru hudu da suka wuce Boko Haram suna shigowa birnin tarayya Abuja a lokacin da suka ga dama.

Tsohon shugaban kasa, Gudluck Jonathan shine ke kan mulki a wancan lokacin.

Da yake magana da yan jaridu bayan ya kai ziyara wasu manyan kafofin yada labarai dake kasar Amurka.

Muhammed ya ce gwamnatin shugaban kasa Muhammad Buhari ta yi nasarar murkushe yan kungiyar Boko Haram.

Ya ce mazauna birnin Maiduguri yanzu haka suna rayuwa cikin jin dadi idan aka kwatanta da shekarun baya.

A cewar kamafanin Dillancin Labaran Najeriya NAN, ministan ya ziraci ofishin jaridar NewYork Times, Washington Post, Washington Times, Voice of America, gidan talabijin na CNN, Aljazeera da kuma ofishin kamfanin Dillancin labarai na Rueters.

Sai dai rahoton da kamfanin Dillancin labarai na Rueters ya wallafa a yan kwanakin nan zai haifar da shakku kan ikirarin ministan na cewa gwamnati ta murkushe yan Boko Haram.

Rahoton na Rueters ya nuna cewa har yanzu ya yan kungiyar ta Boko Haram bangaren albarnawi na cigaba da iko da wasu sassa na jihohin Borno da Yobe.

You may also like