Karo Na Biyu Kenan Gwamnatin Najeriya Tana Cin Amanar Gwamnatin Saudi-ArabiaBabu shakka Allah Ya jarrabi al’ummar Nigeria da miyagun azzaluman shugabanni, wata kila saboda irin laifukan da mukeyi ne sai Allah (SWT) Ya jarrabemu da shugabanni azzalumai barayi maciya amana, don haka akwai bukatar mu gyara halayenmu wallahi. 

Labarin da yaja hankalin mutanen Nigeria a tsakanin kwanakinnan shine batun tallafin kyautar dabino wadda gwamnatin Saudi Arabia ta turo a hukumance ga gwamnatin Nigeria domin a rabawa jama’ar Nigeria kyauta. 

Babu wanda yasan da labarin wannan abin alheri da gwamnatin Saudiyyah tayi ga kasarmu Nigeria sai su a tsakaninsu mahukunta, amma kwatsam kawai sai ga labari ya fito daga mahukuntan Nigeria suna baiwa gwamnatin Saudiyyah hakuri akan cin amanar da sukayi, ta hanyar sayar da dabinon ga mabukata maimakon a bada dabinon kyauta ga jama’ar Nigeria kamar yadda gwamnatin Saudiyyah tace ayi. 

Wannan abin takaici ne da bakin ciki, cin amana ne zalunci da sata, ban taba zaton irin haka zai faru a karkashin shugabancin shugaban kasa Baba Buhari mai gaskiya ba.
Kuma ni dai har yanzu banji wani labarin an kama ‘yan iskan shugabannin da suka sayar da dabinon ba, bamu yafe ba Allah Ya isa har sai sun amayar. 
Jama’a sau biyu kenan gwamnatin Nigeria take cin amanar gwamnatin Saudiyyah
Kundai ji labarin cin amanar da sukayi kwanannan akan dabino kuma cikin azumin watan ramadan ko?.
Sai cin amana ta biyu wacce ta faru akan hanyoyin magance matsalar wutar lantarki a duk fadin Nigeria

Cin amanar dabino ta faru a karkashin shugabancin Baba Buhari (Allah Ya bashi lafiya) wata kila da yana nan a cikin kasa baza’ayi wannan cin amana ba.
Sai cin amana ta biyu wacce ta faru a karkashin shugabancin shugaban kasa marigayi Alhaji Umaru Musa ‘Yar A’dua (Allah Ya jikanshi) akan abubuwan da za’a magance matsalar wutar lantarki a Nigeria
Wannan cin amana ta dabino itace ta tunatar dani cin amanar kayayyakin da za’a magance matsalar wutar lantarki a Nigeria, wanda wannan matsala ta ma fi damun ‘yan Nigeria fiye da tallafin dabino
Kuma duk fadin Nigeria babu wanda ya iya fitowa ya daure ya fallasa yadda mahukuntan Nigeria a wancan lokaci sukaci amanar gwamnatin Saudiyyah akan tallafin magance matsalar wutar lantarki wanda ta baiwa Nigeria kyauta face babban malaminmu masoyi marigayi Ash-Sheikh Abu Abdir Rahman Muhammad Auwal Adam Albaniy Zaria (Rahmatullahi Alaihi), wanda ita wannan fallasa da yayi akan wadanda sukaci amanar Saudiyyah akan tallafin da ta bayar na kayan wutan lantarki, mu masoyansa muke sanyawa a cikin dalilan da yasa aka hallakashi, 
Domin shi Malam Albaniy Zaria shine wanda gwamnatin ‘Yar adua a wancan lokaci ta baiwa kwangilar yin bincike akan matsalar wutan lantarki da hanyoyin da za’a magance, kasancewarsa shima kwararren Engineer ne bayan Malunta ( a shekaran data gabata nayi dogon rubutu mai taken SIRRIN WUTAR LANTARKI) a cikin rubutun na kawo cikekken bayanin yadda akayi gwamnatin Saudiyyah ta tallafawa Nigeria da duk kayayyakin da za’a magance matsalar wutan lantarki a Nigeria wanda Sheikh Albaniy Zaria ya fallasa
Malam Albaniy Zaria yace wallahi duk wani abinda ake bukata a saya wajen magance matsalar wutar lantarki a Nigeria sai dai gwamnatin Saudiyyah ta baiwa Nigeria kyauta, kawai mahukuntan Nigeria zasu biya kudin saka kayayyakin ne, shahararren attajiri Dahiru Mangal da wani babban darakta a ma’aikatar Power Dr Abdullahi Damau sune wadanda shugaban kasa ‘Yar Adua ya wakilta sukaje Saudiyyah suka karbo kayayyakin a hukumance, kuma ‘yar adua ya fitar da kudi kusan naira biliyan 12 domin ayi aikin saka kayayyakin, amma wasu tsinannu barayi maciya amana suka cinye kudin, kayayyakin duk suka batar dasu a cikin kasa, har Malam Albaniy yake cewa watakila Transformer ko wayar wutar lantarki dakaje ka saya a shagon Ikechukwu irinsu ne wanda Saudiyyah ta baiwa Nigeria amma akabi aka sayar
Jama’a ku lura fa, idan har aikin saka kayayyakin wutar lantarkin da saudiyyah ta bayar kudin aikin sakawar zai kai naira biliyan 12, to shi kuma kudin kayayyakin zai kama nawa kenan? 
Amma duk mutanennan sun cinye, Malam Albaniy yace da akazo aka fadawa ‘Yar Adua cewa an wawushe kudin da ya fitar ayi aikin saka kayayyakin da Saudiyyah ta bayar, tun daga nan sai zuciyarshi ta fara samun matsala saboda tsabagen bakin ciki, shine sai ‘Yar Adua ya tura musu EFCC har aka kama Dr Abdullahi da sauransu, kuma yana daga cikin abinda yasa zuciyar ‘Yar adua ta buga ya mutu
Jama’a kun fahimci cewa sau biyu kenan gwamnatin Nigeria taci amanar gwamnatin Saudiyyah?

Insha Allahu idan na samu cikekken lokaci zan sake gabatar da rubutu mai taken SIRRIN WUTAR LANTARKI A NIGERIA domin kuji irin cikekken fallasar da Malam Albaniy Zaria yayi musu

Ba yabon kai ba, wallahi kar ku rena sakonnin mu, muna da burin ganin kasarmu taci gaba
Yaa Allah muna rokonKa duk wani azzalumi barawon shugaba a Nigeria Ka shiryeshi ya tuba, idan ba zai tubaba Yaa Allah Ka batar dasu daga doron duniya

Yaa Allah Ka jikan malaminmu Sheikh Albaniy Zaria

You may also like