
Asalin hoton, Getty Images
Barcelona ta barar da damar bayar da tazarar maki 15 a teburin La Liga, bayan da ta shi 0-0 da Girona ranar Litinin.
Barca ce ta karbi bakuncin Girona a wasan hamayya na Catalonia fafatawar mako na 28 a La Liga.
Robert Lewandowski ya samu damar cin kwallo a minti na hudu da fara tamaula, amma ya buga ta hau kan sama raga.
Golan Girona, Paulo Gazzaniga, wanda ke wasan aro daga Fulham, ya hana kwallo da dama ya shiga ragarsa, har da ta Raphinha, wadda kiris ta fada raga.
Taty Castellanos daga Girona ya buga kwallo zuwa raga daga baya ta yi fadi ta fita waje.
Wasa na uku da Barcelona ta raba maki kenan a bana a La Liga.
Da wannan sakamakon Barcelona tana ta daya a kan teburin La Liga da tazarar maki 13 tsakani da Real Madrid ta biyu.