
Asalin hoton, BBC/Derrick Evans
Mutane 12 ne suka rage wadanda ake danganta su da matan da suka rantse ba su taba saduwa da maza ba a duniya, a yayin da al’adar nan ta yankin Balkan – inda mata ke rayuwa kamar maza – ta zo karshe.
“Gjystina Grishaj ta ce “Albania ta ksance kalma ce ta namiji, ita ce kadai hanyar da za a yi amfani da ita.”
Wata mata ‘yar shekara 23 da ke zaune a wasu tsaunuka a arewacin Albania, ta yanke shawarar cewa za ta sauya rayuwarta.
Ta yi rantsuwa tare da daukar alkawarin cewa za ta karasa rayuwarta a matsayin namiji.
Iyalan Gjystina suna zaune a yankin Malësi e Madhe da ke Lëpushë fiye da shekaru 100.
Wuri ne da yake da tsaunuka, kuma yana daya daga cikin yankunan da har yanzu akwai al’adar burrnesha, wata dadaddiyar al’ada inda mata kan rantse a gaban manyan gari cewa za su yi rayuwa kamar maza.
A kan kira irin wadannan mata da suna burrnseha ko kuma sworn virgins a turance.
“Akwai mutane da dama da ba su yi aure ba a duniya amma kuma ba a danganta su da burrnsehat.
Gjystina, mai shekara 57, ta ce irin wadannan matan sukan sadaukar da rayuwarsu ga iyalansu kuma komai na maza suke yi, babu abin da ke hada su da mu’amala ta maza.
Asalin hoton, Valerjana Grishaj
Ga yawancin matan da aka haifa a da, sauya kansu da dabi’unsu kamar na zama hanya ce ta samun ‘yancin da maza ne kadai suke da shi.
Zama burrnesha, na barin mata su rinka shiga irin ta maza, su rinka dukkan al’amuransu na irin na maza kamar kula da gida da dai makamantansu.
A matsayinta na matashiya, Gjystina, ko kuma Duni, tana son samun cikakken ‘yanci, bayan rasuwar mahaifinta ta yanke shawarar komawa zuwa macen da ba za ta taba tarayya da maza ba domin jan ragamar iyalanta da kuma yin duk wasu ayyukan da maza ne kadai ke yi don ciyar da iyalanta.
Ta ce “Na fito daga gidan da ke fama da talauci, mahaifina ya rasu, mahaifiyata na da ‘ya’ya shida, don na taimaka mata na yanke shawarar zama burrnesha, wato macen da za ta koma kamar maza don na ciyar da iyalaina.”
Tana gidan saukar baki, tana aiki a gona da kuma kula da dabbobinsu.
A matsayinta na burrnesha kuma jagora a gidansu, tana kuma harkar magungunan gargajiya kamar ganyen shayi da sauran mayuka na magani wanda ta gada daga wajen mahaifinta.
Asalin hoton, BBC/Derrick Evans
” A yau, babu macen da ke son zama mace kamar maza wato sworn virgin, in ji Valerjana. Ta ce a yanzu ‘yan mata ba sa tunanin komawa kamar maza.
Ta girma tare da goggonta a Lepushe, Valerjana mata ba su da wata dama ta azo a gani a yankin.
Ta ce ” Zan iya tuna wa a lokacin da nake aji shida na firamare, akwai wata kawata da ta ke aji tara da aka yi wa baiko, a lokacin ba ta wuce shekara 14 ba.
Ta shaida mini cewa mjin da zata aura ba zai barta ta ci gaba da karatu ba kuma dole ta hakura ta bishi a haka, inji ta.
A maimakon Valerjana ta yi auren wuri ko kuma ta koma mace kamar maza, sai ta bar iyalanta ta tafi Tirana, babban birnin Albania wajen goggonta don ta ci gaba da karatu.
Ta ce a Tirana ‘yan mata da mata na da damarmaki, amma a kauye lamarin ya kazanta.
A yanzu ba za a iya cewa ka ainihin kiyasin matan da suka rage a matsayin sworn virgin ba, to amma a yanzu za a iya cewa mutum 12 ne kadai suke rage a wannan yanayi a arewacin Albania da Kosovo.
Tun bayan rushewar gwamnatin kwaminisanci a shekarun 1990, aka fara samun sauye-sauye a Albania, ma’ana mata sun samu ‘yanci.
Valerjana na ganin hakan a matsayin ci gaba saboda al’adar nan ta burrnesha ta fara mutuwar.
Ta ce “A yanzu mu mata ba sai mun yi yakin komawa maza ba, sai dai mu yi yakin samun ‘yanci daidai da su.”
A 2019, wata mai fafutukar kare hakkin mata Rea Nepravishta, ta yi bore ranar mata ta duniya a Tirana.
Ta bi tituna dauke da wani katon allo an zana alamar kalmar burrnesha.
Ta ce ” A harshen Albania, idan muna so mu bayyana mace za mu bayyana ta a matsayin mai jajirciyya.”
Rea ta yi amanna cewa za a samu sauyi mai kyau a kasarta.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, an samu ci gaba sosai a shekarun baya bayan nan wajen shigar mata cikin harkokin siyasa da sauran al’amura a Albania.
A 2017, an samu kashi 23 cikin 100 na mata ‘yan majalisa da kuma kashi 35 cikin 100 na kansiloli.
To amma Rea ta ce har yanzu ana cin zarafin mata a Albania.
Wata kididdiga daga Majalisar Dinkin Duniya, ta ce kashi 60 cikin 100 na matan Albania ‘yan tsakanin shekara 15 zuwa 49 sun fuskanci cin zarafi.
Haka zalika mata na fuskantar wariya ko a wajen rabon gado.
Asalin hoton, BBC/Derrick Evans
Asalin al’adar burrnesha shi ne Kanun, wato tana cikin kundin tsarin mulkin da ake amfani da shi a Kosovo da kuma arewacin Albania a karni na 15, kuma a wannan al’ada ana yi wa mata kallon su dukiyar mjinsu ce.
Ba su da wani ‘yanci na yanke hukunci a kan wani abu da ya nemi su ko kuma su zabarwa kansu rayuwar da suke so.
Idan ana so ayi wa yarinya baiko, to ba a neman shawararta.
Irin wannan shawarar da ake yankewa mata ce ta sa suke komawa matan da ke shan alwashin ba su taba tarayya da maza ba, wato sworn virgin a turance.
Zabin mata na komawa sworn virgin, ba shi da wata alaka da badala, kawai zabi ne na komawa wani jinsi da kuma samun wani matsayi a wajen iyali in ji Aferdita.
To amma komawa burrnesha, hanaya ce ta kaucewa auren hadi.
A karkashin dokar Kanun, zubda jini wata al’ada ce da ake don kare martaba da kimar mutum ko iyali.
Asalin hoton, BBC/Derrick Evans
Ba a tilastawa Gjystina komawa al’adar burrnesha ba, ita ta zabi hakan don sauya rayuwarta, tana ganin cewa maza sun fi mata samun dama a Albania.
Ta ce, akwai wasu damarmaki da mata bata da su, hatta wajen magana ba komai a ke barinsu su fada ba.
Iyalanta musamman, mahaifiyarta bata yi na’am da bukatarta na komawa matana da ke rantsuwa ba za su taba tarayya da maza ba.
A cewarta, sadaukarwar da ta yi kwalliya ta biya kudin sabulu.
To amma ga wasu, su kan zabi koma wa irin matan ne saboda suna ganin maza sun fi mata duk wata dama.
Ga Drande, rungumar wannan al’ada, hanya ce ta jin dadin rayuwa kamar shan sigari da shan barasa da dai makamantansu.
Akwai wani abu da ake sha a Albania, maza ne kadai ke sha.
Drande ya ce wannan abu da mazan ke sha yana kara musu kuzari.
Drande ya ce zabin na bin wannan al’ada ya kara masa kima a garinsu.
Ya ce a kodayaushe ana girmamani kamar yadda ake yi wa maza, ina jin dadi a raina.
Asalin hoton, BBC/Derrick Evans
Ko a yanzu ma a babban birnin Albania, rayuwar mata matasa na da matukar wuya.
Valerjana, ta kirkiri wata manhaja a intanet da take wayar da kan mata da kuma nuna musu ire iren abubuwan da suke ‘yancinsu ne.
Ta ce,” Ina samun sakonni da dama daga maza, wani lokaci ma har da barazanar kisa, wai kawai saboda ina kalubalantar dalilan da ya sa ake tauyewa mata hakki.”
Ta ce a yanzu ba wai sai mata sai rungumi al’adar burrnesha ba, ko kuma sun koma irin matan da ake rantsuwa a kan ba za su taba tarayya da maza ba wato sworn virgin, saboda akwai hanyoyin da za su iya cin gashin kansu.