Karuwar Talauci A tsakanin Palasdinawa Saboda Haramtacciyar Kasar Isra’ila


 

An bayyana Haramtacciyar kasar Isra’ila A matsayin Mai haddasa karuwar talauci a Palasdinu

Kamfanin Dillancin Labarun Palasdinawa ” Ma’a” ya ambato kungiyar kare hakkin bil’adama ta ‘al-mizan’ na dorawa haramtacciyar Kasar Isra’ila alhakin karuwar talauci a tsakanin Palasdinawa.

Rahoton kungiyar kare hakkin bil’adaman ta Palasdinawa wanda aka fitar da shi a ranar fada da talauci ta duniya, ya ci gaba da cewa; siyasar da haramtacciyar Kasar Isra’ila ta ke aiki da ita ce musabbabin karuwar talaucin a tsakanin al’ummar palasdinu.

‘Yan sahayoniya dai suna killace da yankunan Palasdinawa da lalata muhimman cibiyoyinsu da kuma rusa masan’antunsu da kuma gonaki da kasuwancinsu.

Yankin Gaza ya fi fuskantar matsalolin tattalin arziki idan aka kwatanta shi da yankin yammacin kogin Jordan da ke karkashin gwamnatin kwarya-kwaryar palasdinu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like